Ba mu tura jami’an tsaro masarautar Kano ba – Nuhu Ribadu

Ba mu tura jami’an tsaro masarautar Kano ba – Nuhu Ribadu

Ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu ya musanta zargin tura jami’ai zuwa masarautar Kano.

Tun a safiyar ranar Asabar ne Sarki Sunusi Lamido ya samu rakiyar mataimakin gwamna da tawagar gwamnati zuwa masarautar Kano, bayan karɓar takardar maida shi aiki a jiya Juma’a.

Sabon sarki Sunusi Lamido ya zauna a fada bayan da Hakimai da masoya suka kawo masa mubaya’a.

A hannu guda kuma a safiyar Asabar ɗin ne Sarki mai barin gado Aminu Ado Bayero ya iso filin jirgin saman Kano da jami’an tsaro ya kuma zarce gidan sarki na Nassarawa.

KU KUMA KARANTA:Shekara ɗaya tayi wa Tinubu kaɗan ya warware matsalolin da ya gada – Sarki Sanusi

A wata ganawa da manema labarai mataimakin gwamna Injiniya Abdulsalam ya ce abubuwan mamaki na faruwa a safiyar yau kawo yanzu, inda ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musumman a harkokin tsaro suka rako tsohon sarki Kano.

Ya ce abu ne da ba’a taɓa yinsa ba a tarihin Kano, kuma hakan ka iya haifar da fitina da tada zaune tsaye.

A gidan Nasarawa kuwa shima sarki mai barin gado ya ce suna bin umarnin kotu ne kuma babu wanda ya fi ƙarfin hukuma.

A halin da ake ciki dai tuni gwamnan Kano da mai martaba sarki Sunusi da manyan jami’an tsaro suka shiga wata tattauna ta sirri.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *