Ba mu nemi izinin gwamnatin tarayya don ɗaukar makamai ba – FRSC

0
269

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) a ranar Lahadi ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tana neman izinin gwamnatin tarayya domin jami’anta su fara riƙe makamai a wajen aiki.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na FRSC na ƙasa, Marshal Bisi Kazeem ya fitar a Abuja, ya buƙaci jama’a da su yi watsi da rahoton.

“An jawo hankalin hukumar FRSC kan wani rahoto da ke nuna cewa jami’an hukumar na neman izinin gwamnatin tarayya domin jami’an hukumar su dinga ɗaukan makamai zuwa wajen aiki.

“Maganganun kuskuren da wakilin corps Marshal ya yi a wajen bikin faretin na FRSC a garin Kotangora na jihar Neja, bai yi daidai da matsayin shugaban hukumar da jami’an gudanarwar a halin yanzu ba,” in ji Kazeem.

Leave a Reply