Ba mu da shirin ƙara farashin man fetur a kwanan nan – NNPCL

0
239

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗa wa cewa yana shirye-shiryen ƙara farashin man fetur a kwanan nan.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalinsa na X (Twitter a da) ranar Juma’a.

Ya ce, “Saɓanin jita-jitar da ake ta yaɗawa, ba mu da shirin ƙara farashin man fetur.”

NNPCL ya ce har yanzu gidajensa na ci gaba da sayar da man a kan farashi mai rahusa.

A cewar kamfanin, “Ya ku abokan hulɗarmu, mu a gidajen man NNPC muna alfahari da cinikinku, sannan ba mu da shirin sake ƙara farashin man saɓanin yadda ake ta yaɗa wa. Ku yi ƙoƙari ku ci gaba da sayen ingantaccen mai a gidajenmu da ke faɗin ƙasar nan a farashi mai rahusa.

KU KUMA KARANTA: Kamfanin NNPC zai fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

Tun bayan cire tallafin mai a ƙarshen watan mayun da ya gabata dai, NNPCL ya ƙara farashin mai aƙalla sau biyu.

Sai dai tun a farkon makon nan ne dai aka ga galibin gidajen man ’yan kasuwa sun kasance a rufe, sai ’yan tsirari da suke sayarwa a kan farashi mai tsada, yayin da ake fargabar yin ƙarin kuɗin.

Leave a Reply