Ba mu da niyyar kafa sansanin soji a Najeriya – Amurka

0
121
Ba mu da niyyar kafa sansanin soji a Najeriya - Amurka

Ba mu da niyyar kafa sansanin soji a Najeriya – Amurka

Amurka ta sanar da cewar ba ta da wani shiri na kafa sansanin soji a Najeriya, inda ta kuma ce tana aika sojojinta da ta janye daga Nijar zuwa ƙasashen Afirka da suke ƙawance da ita.

Manjo Janar Kenneth P. Ekman, jagoran Dakarun Amurka a Yammacin Afirka da ke ƙarƙashin AFRICOM ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da ‘yan jarida a ƙarshen mako a Abuja.

Bayan amincewa da janye dakarunta daga Nijar baki ɗaya a farkon shekarar nan saboda taɓarɓarewar alaƙar diflomasiyya da gwamnatin sojin ƙasar ta yankin Sahel, an samu wasu rahotanni da ke cewa Amurka za ta mayar da sansaninta zuwa Najeriya.

KU KUMA KARANTA: An yi musayar fursunoni tsakanin Amurka da Rasha

Tuni gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi, wanda Manjo Ekman ya tabbatar da hakan a yanzu.

“Ina son shaida muku cewa babu wasu shirye-shirye na kafa sansanin sojin Amurka a Najeriya, kuma na so na zanta da ku ne saboda batun na da muhimmanci,” in ji Ekman.

Ya ce “Na fahimci yadda wanzuwar sojojin Amurka ke zuwa da amfani da kashe kuɗaɗe, duba ga yanayin da ake ciki, kuma ina son tabbatar muku cewa ba wannan batun ne ya kawo ni nan ba, babu wannan shiri.

Abin da na zo tattaunawa shi ne batun tsaron yankin wanda yake shafar Najeriya.”

Jami’in sojin na Amurka ya ƙara da cewar ya zo Najeriya ne don jin ra’ayin shugabannin soji da na fararen-hula a ƙasar kan ayyukan Amurka na samar da tsaro a yankin.

“Ana buƙatar sauraro, kuma wannan ce gaɓar, wannan ne babban dalilin zuwan. Na fahimci yadda kasancewa ta a nan ke da amfani, ƙari kan ziyarar sauran shugabannin Amurka.

Mataimakiyar Minista Stewart ta zo nan kwanakin baya, inda ta tattauna kan Ma’aikatar Tsaron Amurka da DOD nexus, inda ta taɓo alhakin da ake da shi na amfani da ƙirƙirarriyar basira wajen ayyukan soji,” in ji Ekman.

Ya ci gaba da cewa daga batutuwan da suka tattauna da mahukuntan Najeriya sun haɗa neman mafita ga matsalolin tsaron da ke damun ƙasar, da yadda taimakon tsaro daga Amurka zai kawo sauyi.

Manjo Janar Ekman ya kuma ƙara da cewar tuni aka fara kai sojojin Amurka da aka janye daga Nijar zuwa ƙasashen Afirka da ke makotaka da Nijar, musamman ma Cote d’Ivoire da Benin.

Leave a Reply