Ba mu da labarin rasa rai a lokacin zanga-zanga – ‘Yan sandan Kano
Daga Shafaatu Dauda, Kano
Kwamishinan ‘yan sandan kano ya bayyana haka ne ranar litinin a lokacin ganawarsa da ’yan jarida, inda ya ce rundunar ta kama mutane 873 kan laifin lalatawa da sace dukiyoyin jama’a da na gwamnati a lokacin zanga-zangar.
“A iya bayanan da muke da su, zuwa yanzu ba mu da rahoton asarar rai a yayin gudanar da zanga-zangar,” Cewar CP Salman Dogo Garba.
Iyalan waɗanda suka rasun dai sun bayyana damuwa bisa yadda zanga-zangar da aka shirya ta lumana ta yi ajalinsu, inda suka bukaci a bi musu hakkinsu.
Zanga-zangar lumanar ta rikiɗe zuwa tarzoma ne bayan da ɓata-gari suka ƙwace ta, suka riƙa fasa wurare suna sace-sace, tare da jikkata mutane a sassan jihar ta kano.
KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: ‘Yan sanda a Kano sun cafke mutum 873 da ake zargin lalata dukiyoyi
An yi ɗauki-ba-daɗi tsakanin ɓata-garin da jami’an tsaro a kofar gidan gwamnatin jihar da sauran sassan jihar ta kano, inda aka kama sama da mutum 100.
Kasancewar lamarin ya kai ga gwamnan jihar, Eng.Abba Kabir, sanya dokar hana fita tsawon awa 24, kafin daga bisani aka sassauta dokar.