Ba mu amince Sojojin Najeriya su yaƙi Nijar ba – Majalisar Dattawa

0
295

Daga Ibraheem El-Tafseer

Majalisar dattawa ta yi fatali da yunƙurin ɗaukar matakin amfani da ƙarfin soji a kan Jamhuriyar Nijar.

Majalisar ta yi ƙira ga membobin ECOWAS da sauran shugabanni da su yi tir da juyin mulki a ƙasar tare da tashi tsaye wajen daidaita lamura ta sigar da ya dace.

A cewar majalisar akwai buƙatar ɗaukar matakan laluma da zurfin tunani wajen shawo kan rigimar shugabanci da ke faruwa a Nijar.

A ranar Juma’a ne shugaba Tinubu ya rubuta wasiƙa ga majalisar yana neman amincewarta kan aiwatar da matsayar da shugabannin ECOWAS suka cimma a kan halin da ƙasar Nijar ke ciki.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya har yanzu ba su samu umarnin shiga tsakani a Nijar ba – DHQ

A jawabin ECOWAS da shugabanta, Bola Ahmed Tinubu ya fitar, ya ce ɗaukar matakin ƙarfin soji ne kawai zai kawo ƙarshen juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.

A yayin zaman majalisar a ranar Asabar, Sanata Bamidele Opeyemi, ya bijiro da batun tare da nuna adawa da matakin ƙarfin Soja, inda majalisar ta cimma matsayar ƙin amincewa da matakin tare da neman shugaban Nijeriya da ya ƙara azama wajen ganin an shawo kan rikicin ta hanyar tattaunawa.

Da yake magana bayan zaman da majalisar ta yi a sirrance na tsawon awa biyu, shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya ce ba su amince a ɗauki matakin Soja kan Nijar ba ne saboda kyakkyawar alaƙa da ta jima a tsakanin Nijar da Nijeriya.

“Zaman namu, majalisa ta yi tir da juyin mulkin da ya wakana a jamhuriyyar Nijar.

“Majalisa ta jinjina wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanni ECOWAS bisa ɗaukan matakin gaggawa kan lamarin.”

Ya ce, amma Tinubu ya bi matakin tambayar majalisar domin zuwa ga fagen yaƙi domin aiwatar da matsayar da ECOWAS ta cimma, “Jagorancin majalisa za ta samu shugaban ƙasan domin faɗa masa matakin da ya dace a ɗauka domin shawo kan wannan lamarin domin tabbatar ba a lalata alaƙar da ke tsakanin Nijar da Nijariya ba,” Akpabio ya shaida.

Leave a Reply