Ba Ministar Jin-ƙai ce kaɗai ta aikata almundahanar kuɗi ba – Atiku

0
141

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wasu masu hannu a badaƙalar almundahanar kuɗi da ake zargin ministar jin-ƙai, Betta Edu ta aikata.

Atiku wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jamiyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023, ya bayyana hakan yayin da yake yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan matakin da ya ɗauka na dakatar da ministar jin-ƙa, duk da a cewarsa hakan ma kaɗai bai wadatar ba.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar, inda kuma ya umarci hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta gudanar da bincike a kanta.

Matakin na zuwa ne bayan ya fuskanci ƙiraye-ƙirayen ɗaukar mataki a kanta saboda zarge-zargen tafka almundahana, wanda ministar ta musanta.

Ministar da aka dakatar ta fuskanci gagarumar suka ne bayan kwarmata wasu takardun kashe kuɗi daga ma’aikatarta, waɗanda suka nuna ta bayar da umarni ga babbar akanta ta biya naira miliyan 585 cikin wani asusun ajiyar wata, lamarin da ake zargin ya saɓa ƙa’idojin kashe kuɗi na gwamnati.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya dakatar da Ministar Ma’aikatar Jin-ƙai, Betta Edu

Cikin wata wasiƙar martani da wani mataimakinsa na musamman Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce abin takaici ne ganin yadda shirin da aka kafa da zummar tsamo ’yan Najeriya miliyan 100 daga matsanancin talauci amma kamar yadda ake zargi ya zama saniyar tatsa ga gwamnatocin jam’iyyar APC.

Ya ce, “Ko da yake Tinubu ya cancanci yabo saboda dakatar da Betta Edu, amma muna da yakinin cewa an ɗauki matakin a makare.

“Da farko, ba shi [Tinubu] da wani dalilin wajen naɗa ta a matsayin minista a irin wannan muhimmiyar ma’aikata. Sai dai Tinubu ya fifita siyasa a kan ƙwarewa, lamarin da ya janyo wannan abin kunya.

Leave a Reply