Ba ma ɗaukar ma’aikata – PenCom

0
197

Hukumar fansho ta ƙasa, PenCom, a ranar Laraba, ta nesanta kanta da wata jarida mai cike da ƙarya, tana zargin ta fara ɗaukar ma’aikata a shekarar 2023/2024.

Abdulqadir Ɗahiru a wata sanarwa da ya fitar a Legas, ya ce hukumar ba ta da alaƙa da adireshin gidan yanar gizon: www.recruitmentfile.net da wasu ‘yan damfara suka samar, don cutar jama’a.

“Baddar ta bayyana cewa waɗanda suka cancanta su gabatar da aikace-aikacensu ta hanyar tashar ɗaukar ma’aikata a gidan yanar gizon hukumar.

“An yi ƙira ga jama’a da su lura cewa labarin ƙarya ne kuma babu wani ɗaukan aikin da ake yi.

KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC

“A halin yanzu dai hukumar ta kai rahoton shafin yanar gizon ga hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakin da ya dace.”

Ɗahiru ya ce duk sahihin bayanai game da ayyukan hukumar ana samun su a gidan yanar gizon ta: www.pencom.gov.ng da kuma hanyoyin sadarwar ta: Facebook: @PenCom.gov, da Twitter: @PenComNig.

Leave a Reply