Ba ku da damar ta da zaune tsaye a Najeriya – Akpabio ga masu zanga-zanga
Daga Idris Umar, Zariya
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya gargaɗi masu shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin Najeriya cewa duk da cewa suna da ‘yancin yin hakan, amma ba su da hurumin ta da zaune tsaye a ƙasar.
Akpabio ya kuma zargi ‘yan siyasar da suka sha kaye a zaben da ya gabata da cewa su ne ginshiƙin zanga-zangar neman karɓe gwamnati ta bayan fage.
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana haka ne a yayin rattaɓa hannu kan sabon mafi ƙarancin albashi da shugaba Bola Tinubu ya yi a fadar shugaban ƙasa a ranar Litinin.
Ya ce ya ji daɗin ma’aikacin Najeriya da gyaran mafi ƙarancin albashi na ƙasa da aka yi.
“Wannan babbar rana ce ga ma’aikata a ƙasar. Ba wai kawai muna ninka mafi ƙarancin albashi ba, mun ƙara wani abu a saman.
Da farko Naira dubu 30,000, yanzu ya zama Naira dubu 70,000.
“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen yin ƙira ga masu yunƙurin ta da fitina; cewa kana da haƙƙin yin zanga-zanga.
Haƙƙi ne na asali na ku. Yana nan a cikin kundin tsarin mulki.
KU KUMA KARANTA: Babu barazanar da za ta hana mu gudanar da zanga-zanga – Ƙungiyar Matasan Arewa
“Amma ba ku da haƙƙin ta da zaune tsaye a ƙasar. Bai kamata a mayar da ‘yancin yin zanga-zanga zuwa ‘yancin tayar da hankali ba.
A bayyane yake cewa mutanen da ke bayan wannan suna da tsoro, ba su da fuska sosai.
“Don haka abin da ake nufi shi ne mutane suna shirye-shiryen kwasar ganima da zagayawa da yin abubuwa iri-iri. Inda muke a yau ba mulkin shekara ɗaya ne ya kawo mu ba,” inji shi.