Ba korar Rahama Sa’idu mu ka yi kan TikTok ba, faɗuwa ta yi a jarrabawa — Kwalejin Lafiya ta Kebbi

0
349

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kwalejin koyon aikin jinya ta jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi ta musanta korar ɗalibarta mai suna Rahama Sa’idu bisa dalilin fitowa a kafar TikTok tana baɗala.

Rahama, wata fitacciyar ‘yar Tiktok da Instagram ce, wacce a ke ta raɗe-raɗin cewa makarantar ta kore ta saboda wallafa bidiyoyi a shafukanta na sada zumunta.

Sai dai jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, kwalejin ta ƙaryata jita-jitar, inda ta ce an kori ɗalibar ne saboda rashin bin ƙa’idojin kwalejin.

A cewar kwalejin, an kori ɗalibar daga makarantar ne saboda ta faɗi jarrabawar da ta yi, kuma ta ƙi karɓar zaɓin maimaitawa kamar yadda dokokin makarantar su ka sharɗanta.

“Bisa ga dokokin kwalejin, duk ɗalibin da ya yi sati uku ba a makaranta ko asibiti ba, ba tare da wani dalili na ƙwaƙƙwara ba, to zai maimaita wannan zangon karatu kai tsaye.

KU KUMA KARANTA: Ɗan majalisar wakilai na NNPP da tirabunal ta kora, ya ƙwato kujerarsa a kotun ƙoli

“Rahama Saidu ta faɗi jarabawa watanni 5 da suka wuce, tun daga lokacin ne ta daina zuwa makaranta ba tare da wani dalili ba. Ba ta amince da maimaita zangon karatun ba, ta kuma ƙi amsa dukkanin tambayoyi na jin bahasi da aka riƙa aika mata,” wata sanarwa da makarantar ta fitar ta bayyana.

Sanarwar, duk da haka, ta lura cewa kwalejin ba ta san cewa Rahama ‘yar Tiktok ba ce.

“Saboda haka, duk zarge-zargen da Rahama ta yiwa kwalejin ƙarya ne, maras tushe kuma zargi ne kawai don ɓata sunan kwalejin wanda ya kamata jama’a su yi watsi da su,” in ji sanarwar.

Leave a Reply