Ba kama shugaban ‘yan ƙwadago muka yi ba — ’Yan sanda

0
203

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo, ta ce jami’anta ba kama Shugaban ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero suka yi ba a Owerri, babban birnin jihar.

A ranar Laraba ne shugaban yaɗa labarai na NLC, Benson Upah, ya ce jami’an ‘yan sanda ɗauke da makamai sun yi awon gaba da Ajaero a sakatariyar NLC da ke Imo. 

Ya ce “’Yan sanda ɗauke da makamai sun yi awon gaba da shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajaero, mintuna kaɗan da suka gabata daga sakatariyar NLC a Owerri, sun tafi da shi wurin da ba mu sani ba,” in ji Upah.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Henry Okoye, kakakin rundunar ‘yan sandan Imo, ya ce shugaban NLC ya yi sa’insa da wasu mutane a filin jirgin saman jihar.

Okoye ya ce yunƙurin ɗaukar mataki ne ya sanya ‘yan sanda suka tsare shugaban NLC a hedikwatar ‘yan sandan jihar don ba shi kariya.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun cafke shugaban ƙungiyar ƙwadago na Najeriya

“Bayan samun wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Imo ta gaggauta tura jami’an ‘yan sanda zuwa wurin tare da kai wa shugaban NLC ɗauki zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta jihar domin tabbatar da tsaron rayuwarsa,” in ji kakakin ‘yan sandan.

“Bayan haka kwamishinan ‘yan sanda ya ba da umarnin a kai shi sashen kula da lafiya na ‘yan sanda da ke Owerri, inda za a kula da lafiyarsa sakamakon shirin kai masa harin.

“Don haka an ba shi cikakkiyar kariya da tsaro don ci gaba da sauran ayyukansa na yau da kullum.”

A ranar 30 ga watan Oktoba, ne NLC ta yi alƙawarin za ta dakatar da ayyuka a Imo daga ranar 1 ga watan Nuwamba, domin bayyana rashin jin daɗinta kan take haƙƙin ma’aikata.

Ajaero ya yi zargin cewa gwamnatin Imo ba ta biya wasu ma’aikata albashi na tsawon wata 20 ba.

Leave a Reply