Ba a ba mu kundin hukuncin kotun ɗukaka ƙara ba — NNPP

0
168

Jam’iyyar NNPP ta ce har yanzu Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya ba ta damƙa wa lauyoyinta ainihin kundin hukuncin kotun da ta ƙwace kujerar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ba.

NNPP ta yi korafin cewa jinkirin fitar da ainihin takardar hukuncin na barazana ga ƙoƙarin jam’iyyar na dawo da kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf da kotu ta ƙwace.

Tun a ranar Juma’a da kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin ƙwace kujerar Abba, gwamnan ya yi alkawarin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli tare da ƙiran magoya bayansa da kada su yanke ƙauna daga ɓangaren shari’a.

Sai dai yanzu bayan kwanaki huɗu, shugabancin NNPP na kokawa cewa har yanzu ba a ba wa lauyoyinsu ainihin kwafin hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar ba, ballantana su fara aikin tafiya Kotun Ƙoli.

Muƙaddashin shugaban NNPP na ƙasa, Abba Kawu Ali, ne ya yi wannan ƙorafi a ranar Litinin yana mai cewa rashin ba su ƙundin hukuncin kotun ya fara shiga kwanaki 14 da doka ta ƙayyade da za su iya ɗaukaka ƙarar.

KU KUMA KARANTA: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da Gawuna a matsayin gwamnan Kano

“Abin takaici, wannan yanayi na haifar da zargi an shirya jefa jam’iyyarmu da kuma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da kuma lauyoyinmu cikin damuwa a yayin da lauyoyinmu ke aikin ɗaukaka ƙara domin samun adalci a gaban Kotun Ƙoli,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta gargaɗi cewa za ta sa kafar wanda da magoya bayan jam’iyyu da suka yi yunƙurin gudanar da kowace irin zanga-zanga a jihar kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hussaini Muhammad Gumel, ya gargaɗi masu neman shirya zanga-zanga ko tatttakin a jihar kan hukuncin kotun da cewa duk wanda runduna ta samu yana karya doka a jihar, zai yaba wa aya zaki.

Kakakin rundunar, SP Abdulahi Haruna Kiyawa, ya ce gargaɗin yana da muhimmanci saboda rahotannin da suka samu kan yadda magoya bayan wata jami’iyya ke amfani da wasu hanyoyiyn bayan fage wajen ƙiran jama’a da su fito kan titunan Kano domin zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar.

Kiyawa ya ce, “Mun samu rahoton shirin masu zanga-zangar na tsayar da harkoki da ma tayar da hankali a Kano, shi ya sa muke gargaɗin jama’a da su yi hattara; Duk wanda zai yi zanga-zanga to ya wajibi ne ya yi a bisa yadda doka ta tsara.

“Sannan a sani cewa ranar Alhamsi, 16 ga Nuwamba, 2023, jajibirin zaman kotun ɗaukaka ƙarar, rundunarmu ta yi zama da shugabannin jam’iyyun NNPP da APC inda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya,” a Kano, duk yadda hukuncin kotun ya kasance.

“Sun amince a hana kowane irin taron siyasa, sannan magoya bayansu ba za su yi kowane irin abu mai alaƙa da zanga-zanga ko tattaki ko biki ko lafazi da zai iya tunzura jama’a ko jawo martani ko wata matsalar tsaro ko cin mutuncin ɓangaren shari’a ba.”

A ƙarshe ya shawarci Kanawa da su kwantar da hankalinsu, amma su guji duk wani haramtaccen tattaki ko zanga-zanga ko tashin hankali da aka ƙira su.

Leave a Reply