Ba a ƙara wa shugaban ƙasa, mataimakinsa, zaɓaɓɓun ‘yan majalisa da alƙalai albashi ba – Gwamnatin tarayya

2
239

Mun samu labarin da ke yawo cewa an yi ƙarin kashi 114 cikin 100 na albashin shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, zaɓaɓɓun masu riƙe da muƙaman siyasa na tarayya da na jihohi da kuma jami’an shari’a.

A wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman da yaɗa labarai, Dele Alake, ya ce wannan labari ne marar tushe domin babu inda Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da batun ƙarin albashin, kuma babu inda aka gabatar da wannan ƙudiri a gabansa domin neman yardarsa.

Duk da cewa yana cikin kundin tsarin hukumar tattara kuɗin shiga da tsara kasafin kuɗi ta ƙasa (RMAFC) su ba da shawarar daidaita albashi da alawus ga masu riƙe da muƙaman siyasa da alƙalai, sai dai hakan ba zai iya aiki ba har sai shugaban ƙasa ya yi duba tare da amincewa da shi.

KU KUMA KARANTA: Ya kamata a duba batun ‘mafi ƙarancin albashi’, Tinubu ya gayawa gwamnonin APC

Sannan kuma hukumar RMAFC, ta hannun Manajan Hulɗa da Jama’a, ta mayar da martani kan wannan labari na ƙarya da ake yaɗawa, ta kuma bayyana gaskiyar al’amarin.

Wannan labari mara tushe ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta da kuma wani ɓangare na kafafen yaɗa labarai, wanda hakan ya ƙara haifar da hatsarin da labaran ƙarya ke haifarwa ga al’umma da kuma ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Ba shakka, an ƙirƙiri wannan labarin ƙaryar ne don mugun nufi ga sabuwar gwamnati, da nufin kawo tarnaƙi akan yunƙurin da ake yi na samar da gyara, da kuma kyakkyawar sheda da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da samu a tsakanin ‘yan Najeriya a halin yanzu, sakamakon tafiyar da manufofinta cikin tsari mai inganci da zai samar da ci gaba.

Ya kamata ‘yan jarida, kafofin yaɗa labarai, da jama’a duka su fahimci cewa duk labarin ayyukan gwamnati da batu akan manufofin ta da ba su fito a hukumance ba, labari ne marar tushe da ya kamata a yi watsi da shi.

Ana kuma umartar ma’aikatan watsa labarai, a kowane lokaci, su dinga binciko tushen labaransu don tabbatar da sahihancin labaran da suke yaɗawa, wanda hakan shi ne alamar aikin jarida na ƙwarai.

2 COMMENTS

Leave a Reply