Aƙalla mutane 18 ne suka jikkata a Sri Lanka sakamakon hatsarin motar bas

Aƙalla mutane 18 ne suka jikkata bayan wata motar bas mallakin gwamnati ta kauce hanya ta faɗa cikin wani tsauni da ke Watawala a tsakiyar ƙasar Sri Lanka, da sanyin safiyar Talata.

Kakakin ‘yan sandan Nihal Thalduwa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, motar bas ɗin mai ɗauke da fasinjoji kusan 120 na tafiya zuwa Nuwara Eliya daga Colombo.

An kwantar da waɗanda suka jikkata a wasu asibitocin yankin.

KU KUMA KARANTA: Mutane huɗu sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

Da yawa daga cikin waɗanda suka jikkata sun samu karaya, kuma direban da kwandastan sun samu ƙananan raunuka, in ji kakakin ‘yan sandan.

Kakakin ya ƙara da cewa suna zargin al’amuran fasaha ne suka haddasa haɗarin kuma ‘yan sandan Watawala na ci gaba da gudanar da bincike.


Comments

2 responses to “Aƙalla mutane 18 ne suka jikkata a Sri Lanka sakamakon hatsarin motar bas”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Aƙalla mutane 18 ne suka jikkata a Sri Lanka sakamakon hatsarin motar bas […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Aƙalla mutane 18 ne suka jikkata a Sri Lanka sakamakon hatsarin motar bas […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *