“Azumin Sitta Shawwal: Fa’idodi, sharuɗɗa, da muhimmancinsa a musulunci”
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Bayan wucewar azumin watan Ramadan, Musulmai kan yi wani azumin na kwana shida a cikin watan Shawwal. Shi ne azumin da ake kira Sitta Shawwal, domin dacewa da tarin ladan da ke tattare da su.
Malamai sun bayyana cewa babu laifi ko karhanci a fara azumin Sitta Shawwal daga rana ta biyu na watan. Wannan ya biyo bayan fatawoyin malaman Mazhabar Malikiyya, wadanda suka bayyana cewa azumin kwana shida a watan Shawwal na daga cikin mustahabbai.
KU KUMA KARANTA:Daga fara Azumin Ramadan, mutane 11 ne suka musulunta a wajen tafsirin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Malaman addinin Musulunci sukan ambato wani Hadisi daga Manzon Allah (S.A.W) da ke cewa duk wanda ya azumci watan Ramadan sannan ya ƙara da azumin kwana shida cikin watan Shawwal, to za a rubuta masa ladan wanda ya shekara yana azumi.
Malam Nafi’u Muhammad Gezawa wani malamin addini a Kano ya ce ana so mutum ya fara biyan bashin azumin da ake bin sa, kafin yin Sitta Shawwal, matuƙar zai iya yin su kafin ya yi Sitta Shawwal.
Amma ya ce matuƙar azumin da ake bin mutum yana da yawa, ta yadda ba lallai ne ya iya biya gaba ɗaya a watan Shawwal ba, to ya fara yin na Sitta Shawwal ɗin, kasancewar na Sitta Shawwal ɗin suna da ƙayyadajjen lokacin.