Daga Sa’adatu Maina, Damaturu
Ambaliyar ruwa ta zama ruwan dare ga al’ummar Sumsumma da ke ƙasa da kilomita 2 daga Gidan Waziri Ibrahim Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe.
Al’ummar yankin sun sha kukan neman kai masu ɗauki har zuwa ‘yan kwanakin nan da Gwamnatin Jihar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mai Mala Buni, ta sanya al’ummar cikin kasafin ta na shekarar 2023.
Hakan ya bai wa mazauna ‘yankin sabon fatan cewa ambaliyar ruwa da ta katse duk wata hanyar da ta haɗa al’umma da sauran yankunan Damaturu da kewaye za ta zama tarihi nan ba da jimawa ba.
KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya ƙaddamar da hanyar mota mai nisan kilomita 34
Ambaliyar dai, baya ga hana jama’a shiga ko fita daga yankin, ta kuma yi barazana ga wasu gine-ginen da suke zaune a kusa da hanyar ruwa inda a wasu lokutan ruwan ya mamaye gine-ginen nasu yana fatattake su.
A safiyar Asabar 1 ga Afrilu, 2023 mazauna ƙauyen sun wayi gari cikin farin ciki da annashuwa saboda an fara aikin gina magudanar ruwa a yankin.
Sun yabawa Gwamnatin Mai Mala Buni a yanzu bisa wannan karimcin tare da nuna cewa aikin zai magance matsalolin da suke fuskanta a duk shekara.
Mazauna yankin sun kuma bayyana fatan cewa za a kammala aikin kafin zuwan damina.
[…] KU KUMA KARANTA: Ayyukan Hanya: Mazauna ƙauyen Sumsumma sun nuna farin cikin su kan yadda Buni ya shiga tsakani […]
[…] KU KUMA KARANTA: Ayyukan Hanya: Mazauna ƙauyen Sumsumma sun nuna farin cikin su kan yadda Buni ya shiga tsakani […]