ASUU ta fara haɗa kan mambobinta domin fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya

0
126
ASUU ta fara haɗa kan mambobinta domin fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya

ASUU ta fara haɗa kan mambobinta domin fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta fara hada kan mambobinta a dukkan jami’o’in kasar domin fara yajin aikin kasa baki daya da ta tsara.

Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan shiru da gwamnatin tarayya ta yi duk da sanarwar da aka aika wa hukumomin da suka dace, ciki har da ministocin kwadago da ilimi.

DAILY TRUST ta rawaito cewa Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, a wata wasika da aka fitar ranar 5 ga Oktoba, 2025, ya bayyan cewa babu wani ci gaba da aka samu wajen magance matsalolin da suka dade suna janyo sabani tsakanin gwamnati da kungiyar.

KU KUMA KARANTA: Bai kamata ku tafi yajin aiki ana tsaka da tattaunawa ba, Gwamnatin tarayya ga ASUU

Ya ce majalisar zartarwa ta ASUU ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 14 don kammala yarjejeniyar da aka tsara tun watan Fabrairu, 2025, sannan za ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu idan ba a dauki mataki ba.

ASUU ta ce manufar yajin aikin ita ce tilasta gwamnati ta sanya hannu da aiwatar da sabuwar yarjejeniya, da kuma sake farfado da tsarin jami’o’in kasar domin gogayya da sauran kasashe.

Leave a Reply