Arsenal na neman ɗan wasan Atalanta, Ademola Lookman

0
79
Arsenal na neman ɗan wasan Atalanta, Ademola Lookman

Arsenal na neman ɗan wasan Atalanta, Ademola Lookman

Rahotanni na cewa Arsenal ta shirya miƙa gagarumin tayin sayo ɗan wasa ɗan asalin Najeriya, Ademola Lookman, wanda ke taka leda a Atalanta ta Italiya.

Tayin zai ƙunshi maƙudan kuɗi da cikon ɗan wasa, don tabbatar da ɗauka matashin ɗan wasan da ya taimaka wa Atalanta lashe kofin Turai na Europa, wanda shi ne kofi na farko da suka ci tun 1963.

Ademola Lookman shi ne ɗan wasan da ya kafa tarihin cin ƙwallaye uku a wasan ƙarshe na gasar Europa ta bana, inda Atalanta ta doke bayer Leverkusen.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barcelona ta sayi ɗan wasa mai shekaru 26, Dani Olmo

Sai dai Arsenal na fuskantar hamayya daga wasu ƙungiyoyin gasar Firimiya, da kuma hamshaƙiyar ƙungiyar nan ta Faransa, Paris Saint-Germain, duk da rahotanni sun ce ba a samu ƙwaƙƙwaran tayi daga PSG ba har yanzu.

Lookman ya ɗau aniyar barin Atalanta a bazarar nan, inda shafin Sportitalia suka ce Arsenal na shirin miƙa gagarumin tayin da zai kai fam miliyan 42.5 (dala miliyan 55.7), gami da wasu ƙare-ƙare.

Cikin ƙare-ƙaren akwai cikon ɗan wasa da ake tunanin zai zamo Jakub Kiwior, wanda zai rage adadin kuɗin da Arsenal za ta kashe. Haka kuma, idan cinikin bai yiwu ba, akwai yiwuwar su nemi aron sa ganin kakar cinikin ‘yan wasa na dab da ƙarewa.

Lookman bai buga wasan farko da Atalanta ta buga ba a gasar Serie A ranar Litinin tare da Lecce, kamar yadda ɗan wasan ya nema, cewar shafin Goal.com.

Bugu da ƙari, ɗan wasan mai shekaru 26 ya ƙi shiga atisayen da ‘yan ƙungiyarsa suka yi ranar Laraba, domin nuna matsin lamba kan ciki masa burinsa na barin Italiya.

Leave a Reply