Argentina zata sanya hoton Messi a takardun kuɗi

0
514

Rahotanni sun ce babban bankin ƙasar Argentina na shirin sanya hoton Lionel Messi a kan takardar kudin ƙasar peso 1000.

Ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai, ya jagoranci Argentina zuwa wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya, inda ta samu nasara a kan Faransa da ci 4-2 a bugun fenareti, kuma bikin murnar nasarar bai ƙare ba a ƙasar da ke Latin Amurka.

Bajintar da Messi ya taka a gasar da aka kammala kwanan nan, ya ci gaba da jan hankalin jama’a da yawa, inda wasu ke yi masa lakabi da GASKIYAR KOWA.

KU KUMA KARANTA:Yadda Argentina ta lashe kofin duniya bayan ta doke Faransa

A cewar jaridar El Financiero, jami’an babban bankin ƙasar na nazarin hanyoyin da za su bi wajen bikin naɗin sarautar tawagar Tango mai dimbin tarihi a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar, kamar yadda ya faru bayan lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 1978, inda aka ba da tsabar kuɗi don bikin tunawa da nasarar.

Jaridar ta nuna cewa ɗaya daga cikin zaɓin babban bankin Argentina shine buga hoton Messi akan peso 1,000, inda jami’ai a Argentina ke son nuna lamba “10”, wanda ya fara da lamba 1000, da kalmar ” La Scaloneta” an rubuta, wanda ke nuna alamar nasarar kocin ƙungiyar,Lionel Scaloni.

Leave a Reply