No menu items!

Sample Page Title

Date:

APC ta musanta cewa Ganduje ya sha da ƙyar a Gombe

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jamiyyar APC ta musanta labarin da ake yadawa cewa shugaban Jamiyyar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sha da kyar a wajen babban taronta na shiyyar Arewa maso Gabas da aka gudanar a ranar Lahadi a jihar Gombe.

Kakakin jamiyyar na Kano Ahmad Aruwa ne ya karyata faruwar lamarin tare da cewa kin kiran sunan shettiman ba wani laifi bane, kuma ba sabon abu bane.

“Tuni muka gano yunkurin ‘yan kwankwasiyyar na fakewa a bayan kashim Shettima domin tayar da fitina a jamiyyar, saboda yadda suka ga shettiman na shiga al’amuransu.” a cewar sa.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta karyata zargin ciwo bashin Dala Miliyan 6.6 da wasu ƴan APC suka yi mata

Wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, anga jami’an tsaro na kokarin kare jama’ar dake sowa, dai dai lokacin da Gandujen ke barin wurin taron, abin da wasu ke fassarawa da boren ‘yan jamiyyar bayan sun zargi Gandujen da gaza anbatar sunan Kashim Shettima a matsayin mataimakin Tinubu a zaben 2027.

Rahotanni na cewa ‘yan jamiyyar a arewa maso gabas sun fusata ne bayan tsallake sunan Kashim Shettima wanda dan asalin yankin ne, yayin jaddada takarar Tinubu a 2027, abinda suka fassara a matsayin wata makarkashiya ta kokarin sauya Shettiman a zaben 2027.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...