APC da NNPP sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a Kano

0
156

Jam’iyyun APC da NNPP a Kano sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a kan hukuncin da Kotun Ƙoli za ta yanke kan zaɓen gwamnan jihar.

Shugabannin jam’iyyun sun ƙulla yarjejeniyar ne a hedikwatar rundunar ’yan sandan jihar Kano a gaban kwamitin shugabannin hukumomin tsaro.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Usaini Muhammad Gumel, ya ce shugabannin jam’iyyun sun sabunta alƙawarinsu na tabbatar da zaman lafiya a lokacin da kotu ta sanar da hukuncin da ta yanke da kuma a yayin bikin murnar nasara.

KU KUMA KARANTA: NNPP ta shirya ƙawance da jam’iyyun adawa

Ya ce taron ya tattauna kan wasu miyagun ’yan siyasa da ke yunkurin haɗawa tashin hankali a jihar, sannan ya yaba wa shugabannin APC da NNPP kan yadda tsayuwarsu a karo na bisa alƙawarin da suka ɗauka da farko na zaman lafiya.

Usaini Gumel ya ce taron ya kuma tattauna kan matsalar shugabanci a cikin jam’iyyun biyu a wasu ƙananan hukumomin jihar.

Leave a Reply