Anyi inkwankulusib a zaɓen Adamawa

2
406

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta bayyana zaɓen gwamnan jihar Adamawa da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba, wato inkwankulusib

Rahotanni sun nuna cewa ‘yar takarar gwamnan na jam’iyyar APC a jihar, Sanata Aishatu Ɗahiru da aka fi sani da Binani ta samu ƙuri’u 390,275 yayin da gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri, ɗan takarar jam’iyyar PDP, ya samu ƙuri’u 421,524.

Sai dai hukumar INEC ta bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba saboda tazarar ƙuri’u.

Ya zuwa yanzu dai an bayyana sakamakon zaɓen gwamnoni 20, kuma jam’iyyar APC ce ke kan gaba da jihohi 14, yayin da jam’iyyar PDP ke da jihohi biyar sai kuma jam’iyyar NNPP da ta sami jiha ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Yadda Abba Kabir Yusuf na NNPP ya lashe zaɓen Kano

Hakazalika hukumar zaɓe ta ayyana rashin kammala zaɓen a Kebbi yayin da aka daƙatar da tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihohin Abia da Enugu.

A hukumance, gwamnoni tara daga cikin 11 da suka nemi sake tsayawa takara a zaɓen ranar 18 ga watan Maris da aka gudanar a faɗin Najeriya a yammacin Afirka, INEC ta ayyana a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen da za su sake komawa kan karagar mulki na tsawon shekaru hudu kowanne.

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun, Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, Gwamna Abdullahi Sule Jihar Nasarawa, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi da Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe waɗanda dukan su suka kai bantensu.

2 COMMENTS

Leave a Reply