Ana zargin wata ɗaliba da hayar ‘yan daba su kai wa wani Malamin Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano hari

0
33
Ana zargin wata ɗaliba da hayar 'yan daba su kai wa wani Malamin Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano hari

Ana zargin wata ɗaliba da hayar ‘yan daba su kai wa wani Malamin Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano hari

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Wata ɗaliba da ke karatu a Kwalejin kimiyya da fasaha ta Jihar Kano wato Kano State Polytechnic, wadda aka ɓoye sunanta ana zarginta da sa ɗan daba ya kai wa lakcara mai suna, Aliyu Hamza Abdullahi, a ranar Talata, 14 ga Janairu, 2025.

Malamin, wanda shi ne exam officer na sashen, an ce dalibar ta sa wa saurayinta ya kai masa hari.

Lamarin ya faru ne bayan dalibar ta nuna rashin jin daɗi da sashen da aka ba ta, inda ta nemi a canza mata zuwa wani sashe daban. Sai dai, makin ta ba su kai matakin da ake buƙata don samun gurbin karatu a sabon sashen da ta nema ba.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kwalejin, Auwal Ismail Bagwai, ya tabbatar da harin a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa, “harin ya faru ne yayin da malamin ke kula da ɗalibai a ofishinsa da misalin ƙarfe 2 na rana a ranar Talata.

Dalibar ta shiga ofishin tare da saurayinta, tana zargin malamin da zama cikas ga canjin da take nema. Daga nan saurayin ya fito da wuka ya kai wa malamin hari.

KU KUMA KARANTA:’Yan daba sun kashe abokin ango a wurin taron ɗaurin aure

Bagwai ya ƙara da cewa, “malamin ya samu raunuka a hannuwansa yayin da yake ƙoƙarin kare kansa. Sauran ɗalibai da ke cikin ofishin sun yi tsaye suka hana hari, lamarin da ya sa waɗanda suka kai harin suka gudu daga wurin.”

Bayan harin, an garzaya da malamin asibiti don samun kulawar likitoci.

Daga bisani jami’an tsaron makarantar sun tafi unguwar Dorayi, inda dalibar ke zaune, domin cafke ta da saurayinta. Sai dai, lokacin isowarsu, dalibar ta gudu cikin gidanta, sannan wasu matasa dauke da makamai suka fito suka kai wa jami’an tsaro hari.

Bagwai ya tabbatar da cewa, “hukumomin tsaro suna ci gaba da bincike a kan lamarin, kuma malamin da ya ji rauni yana karɓar magani a asibiti.”

Wannan lamari ya janyo damuwa kan tsaro a cikin makarantu da kuma yadda za a magance irin waɗannan matsaloli a

nan gaba.

Leave a Reply