Ana zargin sojojin Chadi da kashe ɗimbim masunta a Najeriya

0
39
Ana zargin sojojin Chadi da kashe ɗimbim masunta a Najeriya

Ana zargin sojojin Chadi da kashe ɗimbim masunta a Najeriya

Ana zargin rundunar sojin kasar Chadi da kisan dimbin masunta a Najeriya a yayin da suke harin masu ikrarin jihadi, kwanaki bayan da mayakan Boko Haram suka hallaka mutane 40 a wani sansanin sojin Chadi, kamar yadda masunta da masu adawa da kungiyar ‘yan jihadin Boko Haram suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP a jiya Alhamis.

Rundunar sojin Chadin ta kaddamar da wani hari ta sama da ya gigita tsibirin Tilma a yankin Kukawa dake bangaren Najeriya na tafkin Chadi a Larabar da ta gabata a yayin da masuntan ke kokarin tattara kifin da suka kama, a cewar majiyoyi.

Wasu kungiyoyi 2 dake fafutuka da makamai masu taimakawa sojin Najeriya yakar masu ikirarin jihadi a yankin sun shaidawa AFP cewa ruwan bama-baman ya hallaka masunta da dama.

KU KUMA KARANTA:Harin Boko Haram ya kashe sojojin ƙasar Chadi sama da 40

“Harin da wani jirgin saman yakin rundunar sojin chadi ya kai a tsibrin tilma ya hallaka dimbin masunta,” a cewar Babakura Kolo, shugaban kungiyar masu yaki da Boko Haram.

“Jirgin ya yi kuskuren daukar masuntan a matsayin ‘yan ta’addar Boko Haram din da suka kaiwa wani sansanin sojin Chadi hari a Lahadin data gabata,” a cewar Kolo.

Wani janar din sojan Chadi da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa AFP da cewar “an kai harin ne akan tsibiran dake kan iyakar Najeriya da Nijar.”

Galibin masuntan da harin ya rutsa dasu sun fito ne daga garuruwan Baga da Doron Baga da Duguri dake gabar tafkin Chadi, a cewar wani mai adawa da masu ikirarin jihadi, Ibrahim Liman.

Leave a Reply