Ana zargin sabuwar ƙungiyar ACHAD da safarar mutane a jihar Filato

0
19
Ana zargin sabuwar ƙungiyar ACHAD da safarar mutane a jihar Filato

 

Ana zargin sabuwar ƙungiyar ACHAD da safarar mutane a jihar Filato

Wace ƙungiya ce ƙungiyar ACHAD kuma mece ce alaƙar ta da safarar mutane a jihar Filato

A makon jiya ne hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta bayyana ɓullar wata sabuwar ƙungiya mai suna ACHAD Life Mission International wanda shelkwatar ta take jihar Kaduna.

Wata sanarwar da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa shugaban kungiyar Mr. Yokana, yana zaune ne a birnin Jos, a jahar Filato.

Sanarwar mai sanya da sa hannun wani babban jami’in shige da fice, A. A. Aridegbe, ta alakanta kungiyar da fataucin mutane da tattara yara da rarraba su a ciki da wajen Najeriya.

Wannan ne ya sa wakiliyar Muryar Amurka a Jos Zainab Babaji, ta bukaci kwamishinar harkokin mata da walwalar jamma’a ta jahar Filato, Caroline Dafur tayi mata karin bayani akan yadda matsalar safarar mutane take a jahar Filato.

KU KUMA KARANTA:‘Yansanda sun kama Muhyi Magaji, shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar Kano

Zainab, ta kuma ruwaito cewa, darekta a wata hukumar tsaro mai zaman kanta, Scottbrian Global Security Services, Honarabul Solomon Nandy Chendan, ya ayyana sanarwar da ta fito daga hukumar shige da ficen Najeriyar akan bullar kungiyar a matsayin mara tushe.

Shi kuma Mr. Jonathan Gukut, cewa yayi lamarin safarar mutane a jahar Filato abin a duba ne da idon basira.

Wakiliyar ta mu ta ruwaito cewa, duk kokarin ji daga hukumar shige da fice a jahar Filato ya ci tura, duk da sakon kar ta kwana da ta aike wa mai magana da yawun hukumar.

Sannan, duk binciken da tayi don samun karin bayani daga daidaikun mutane a cikin garin na Jos, a game da kungiyar ACHAD Life Mission International, babu wanda yace ya san da zaman wannan kungiyar.

Leave a Reply