Ana zargin kwamishina a Kano ya fitar da Naira biliyan 1.17 na kwangilar bogi
Daga Jameel Lawan Yakasai
Kwamishinan raya karkara na Kano, Abdulkadir Abdulsalam, ya shiga zargin badakalar kudi da ake cewa ta kai naira biliyan 6.5, bayan amsarsa kan wati kwangilar bogi da ya sa hannu a kai.
Jaridar Neptune Prime ta tattaro daga jaridar Premium Times cewa Abdulsalam ya amsa fitar da sama da naira biliyan 1.17 a watan Nuwamba 2023, abin da aka bayyana a matsayin tushen badakalar.
Rahoton ya kuma ce an bi ta hannun kamfanoni na bogi da ‘yan canji wajen karkatar da kudin, har ma aka bai wa wasu mutane dala miliyan daya a Abuja.
KU KUMA KARANTA: Na yi murabus ne domin maslahar al’ummar jihar Kano – Kwamishinan Sufuri
Rahoton ya nuna Hukumar ICPC ta riga ta karbo naira biliyan 1.1 daga cikin kudaden, yayin da kotu ta kwace karin naira miliyan 142 daga asusun da ake alakanta da Daraktan Fadar Gwamna Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Rogo.
Sai dai wata kotu a Kano ta bayar da umarnin dakatar da ICPC da EFCC daga ci gaba da bincike, lamarin da kungiyoyin farar hula suka soki.









