Ana zargin Amarya da yiwa angonta yankan Rago a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Ana zargin wata amarya da amfani da wuka wajen yanka Angonta har Lahira a Unguwar farawa da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, a daren Talata nan bayan da ta fara da bashi guba.
Auran wanda na zumunci ne an daura shi a lahadin da ta gabata ne, inda aka yi zargin dama can ba soyayya amma aka rarrashi angon ya amince.
KU KUMA KARANTA:‘Yansanda a Jigawa sun kama ango da abokansa bayan mutuwar amarya
Wakilin Jaridar Neptune Prime ya rawaito cewa yanzu haka tuni jami’an tsaro suka tafi da amaryar, bayan da matasan unguwa suka yi yunkurin daukar doka a hannunsu, amma saidai kawo yanzu ba’a bayyana inda jami’an tsaron suka ajiyetaba sabo da gudun bore daga matasan yankin.









