Ana zaɓen shugaban ƙasa a Chadi

0
83

A yau Litinin ne al’ummar ƙasar Chadi suka fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen Shugaban Ƙasa, a karo na farko cikin shekara uku bayan ƙwace mulki da sojoji suka yi.

An buɗe rumfunan zaɓen ne da misalin ƙarfe 7 na safe agogon ƙasar, inda za a rufe su da ƙarfe biyar na yamma, kuma mutum miliyan 8.5 ne suka yi rajistar zaɓen.

Sai dai tun a jiya Lahadi ne sojoji suka kaɗa nasu ƙuri’un.

Ana sa ran sakamakon farko-farko zai samu zuwa ranar 21 ga watan Mayu, yayin da illaharin sakamakon zai samu ranar 5 ga watan Yuni.

Idan har babu ɗan takarar da ya yi nasara da samun kashi 50 cikin 100 na zaɓen, to za a je zagaye na biyu ranar 22 ga watan Yuni.

Masu sharhi sun ce shugaba mai ci Mahamat Idriss Deby, wanda ya karɓi mulki bayan da ƴan tawaye suka kashe mahaifinsa Idriss Deby da ya shafe tsawon shekaru yana mulki, a watan Afrilun 2021, ga alama shi ne zai yi nasara a zaɓen, duk da cewa babban abokin karawarsa yana samun magoya baya fiye da yadda aka yi tsammani a yayin yaƙin neman zaɓe.

KU KUMA KARANTA: Amurka za ta janye dakarunta daga Chadi

A cikin alkawuransa na yaƙin neman zaɓe, Deby ya ce zai ƙarfafa tsaro da ƙarfafa doka da kuma ƙara samar da wutar lantarki.

Zaɓen dai ya zo daidai da janyewar sojojin Amurka na wucin gadi daga kasar Chadi, wani muhimmin ƙawancen Ƙasashen Yammacin Duniya a yankin yammacin Afirka da kuma tsakiyar Afirka da Rasha ke neman samun ƙarfin faɗa a ji a wajen.

Tun lokacin da ya maye gurbin mahaifinsa a kan mulkin kasar ta yankin Afirka ta Tsakiya, Deby ya ci gaba da kasancewa ƙut-da-ƙut da ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka wato Faransa.

Yayin da sauran kasashen yankin Sahel da ke karkashin mulkin soja da suka hada da Mali da Burkina Faso da Nijar suka shaida wa Faramasa da sauran Ƙasashen Yammacin Duniya da su janye daga gare su, inda suka koma wa neman goyon bayan Rasha, ita kuwa Chadi har yanzu akwai sojojin Faransa masu yawa a cikinta.

Sai dai Amurka ta sanar da janye akalla wasu sojojin na wucin gadi a watan da ya gabata, inda ta ce za ta ci gaba da duba ayyukan tsaro bayan zaben.

Zaɓen na ranar Litinin ya jawo an samu ɓaraka a tsakanin Deby da firaministansa Succes Masra, wanda a baya abokin hamayyar siyasa ne da ya yi gudun hijira a shekarar 2022 amma bayan shekara guda aka ba shi damar komawa ƙasar.

Haka kuma akwai tsohon Firaminista Albert Pahimi Padacke da wasu ‘yan takara bakwai da ke fafatawa a zaɓen.

Shi kuwae Yaya Dillo, ɗan siyasar adawa da aka yi tsammanin zai fafata da Deby duk da cewa sun fito daga ƙabila ɗaya, an harbe shi har lahira a babban birnin N’Djamena a ranar 28 ga watan Fabrairu, ranar da aka saka ranar zaɓen.

Padacke ya zargi Masra da hada kai da Deby. Amma shi ma Masra yana da tasa jama’ar da yawa da suka halarci gangaminsa.

Wasu ‘yan adawa da kungiyoyin farar hula sun yi kira da a ƙaurace wa zaɓen, saboda fargabar yiwuwar za a yi maguɗin.

Hakan ya haifar da fargabar yiwuwar tashin hankali. Baniara Yoyana, wani tsohon minista kuma alkali ya ce “Wannan zaben shugaban kasa yana da matukar muhimmanci ga kasar nan, domin al’ummar kasar baki daya na fatan ya kawo sauyi. Dole ne a yi zaɓen cikin gaskiya da sahihanci don kauce wa duk wani hadarin da zai iya haifar da rikici.”

Leave a Reply