No menu items!

Sample Page Title

Date:

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana damuwa kan yadda ake tsananin buƙatar man fetur saboda gudanar da ayyukan asibitoci da samar da ruwan sha a Gaza.

Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta yi koken ne yayin da manyan tankokin mai ke tunkarar kan iyakar Masar da Gaza, wanda ta ce har yanzu ba a shigar da mai cikin Gaza ba.

Ofishin Kula da Ayyukan Jinƙai na MDD ya ce ya zama wajibi a buƙaci man, kuma rashinsa ka iya kawo rashin tsaftataccen ruwan sha a Gaza, saboda cibiyoyin bayar da ruwan sha da famfuna ba za su yi aiki ba idan babu man fetur.

Yayin da tankokin ke ci gaba da jiran izinin shiga Gaza bari mu duba dalilan da ya sa ake buƙatar man a Gaza, da wuraren da ke buƙatarsa.

Haka kuma ana buƙatar man domin kunna injunan bayar da wutar lantarki a asibitocin yankin.

A makon da ya gabata ne ƙungiyar agaji ta Red Cross ta yi gargaɗin cewa asibitocin Gaza na cikin hatsarin komawa ‘mutuware’ (ɗakin ajiye gawarwaki) idan ba su samu wutar lantarki ba.

KU KUMA KARANTA: Motocin kayan agaji sun fara shiga zirin Gaza

Cibiyoyin lafiya na cikin mawuyacin halin tun bayan ta Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Gaza, yayin da take yi wa yankin luguden wuta ta sama da makaman atilare.

A wani mataki na mayar da martani kan mayaƙan Hamas waɗanda suka kai hari Isra’ila mako biyu da suka gabata tare da kashe mutum 1,400.

Isra’ila ta ce ba za ta mayar da wutar lantarki zuwa Gaza ba, har sai Hamas ta sako mutanenta fiye da 200 da tayi garkuwa da su a lokacin harin.

To amma a jiya Isra’ila ta amince da barin manyan motoci 20 ɗauke da kayan agaji sun shiga Gaza bayan shafe kwanaki ana tattaunawa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...