Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane dubu ɗari uku da arba’in ne aka tilastawa barin muhallinsu, yayin da Isra’ila ke ci gaba da a Gaza don mayar da martani ga harin da Hamas ta kai mata ranar Asabar.
Isra’ila ta hana mutane fita ta ko ina, duk da cewa wasu sun yi nasarar tsallakewa daga yankin.
Isra’ila ta katse wutar lantarki da ruwan sha daga shiga Gaza.
Sai dai kuma, ƙasashe da ƙungiyoyi na ci gaba da ƙiran a samar da yanayin kai tallafi Gazar da kuma bai wa ‘yan gudun hijira damar ficewa.
Hukumomi a Masar sun ce an fara tattaunawa don ganin an ƙulla yarjejeniyar kai ɗauki ga mutanen da yaƙin ya ritsa da su.
KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta ba da umarnin a datse wuta da ruwa a Gaza
Amurka ma ta ce tana tattaunawa da Isra’ila a kan yadda za ta taimaka wajen kwashe fararen hula daga Gaza, bayan shafe kwana biyar Isra’ilan tana luguden wuta a kan garin.
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce dole ne a bayar da damar shiga da muhimman kayan buƙata ga mutanen da ke Gaza.
Scott Paul na ƙungiyar agaji ta OXFAM ya ce abubuwan da ke faruwa a Gaza basu da daɗin ji.
Ya ce ‘’fatan mu shi ne masu faɗa a ji, a duniya za su saurari muryoyin mutanen da lamarin ya ritsa da su, su kuma dubi hotunan da suka bayyana na irin wahalar da ake ciki. Yanzu haka yanke lantarki da ruwa da aka yi daga yankin ya shafi duk wanda ke zaune a Gaza. Mutane fiye d miliyan ɗaya ne ke buƙatar abinci… wannan ba labari mai kyau bane’’.
A ɓangare guda kuma rahotanni na cewa dakarun Isra’ila na ci gaba da matsawa kusa da Gaza, a wani ƙoƙari na afkawa ciki ta ƙasa, bayan hare-haren sama.