Ana lalata mutuncin bil’adama a Gaza – Ministan Turkiyya
Ministan Lafiya na Turkiyya ya ce ana lalata mutuncin bil’adama a Gaza a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare ba kan fararen hula ba har ma da cibiyoyin kiwon lafiya.
A wani taron Majalisar Lafiya ta Duniya (WHA) a Geneva, Fahrettin Koca ya ce “A Gaza, ana lalata mutuncin bil’adama a gaban dukkan idanunmu, ana yi mata rugu-rugu.”
KU KUMA KARANTA: An yi zanga-zangar neman ƙasashen Musulmai su tura sojoji don taimaka wa Falasɗinawa a Gaza
“An ga cewa ƙasashen da ke iƙirarin ci gaba su ne a baya sosai a fannin darajta dan’adam, sun gwammace su yi shiru yayin da ake kashe yara da jarirai da hanyoyin a salon da ake tunanin ya gushe a duniya,” in ji shi. Ya ƙara da cewa:
“Wadanda ake kiran sun fi kowa ci gaba a fannin dimokuradiyya su ne masu ƙin mayar da hankali kan kukan al’umma”.
“Dukkanmu mun kasance fursunonin wannan baƙin tarihi” ya ce.