Ana kukan ƙarancin wutar lantarki a Afirka ta kudu

0
303

Kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasar Afirka ta kudu wato Eskom, ya yi gargaɗin sake samun yankewar wutar lantarki a watanni masu zuwa a ƙasar.

Shugaban riƙo na kamfanin, Calib Cassim ya ce wannan lokacin sanyin zai kasance mai matuƙar wahala a yankin kudancin ƙasar.Matsalar rashin lantarki ya sake tsanani a cikin shekarar da ta gabata.

KU KUMA KARANTA: Hukuma wutar lantarki ta nemi afuwar kwastomomin ta na Kano

Domin shawo kan wannan ƙaranci na lantarki, Eskom ya fito da tsarin taƙaita bai wa mutane wuta. Inda ake shafe tsawon awa 12 ba tare da samun wutar lantarkin ba.

Ana alaƙanta lamarin da ƙarancin samun masu saka hannun jari a fanin makamashi a ƙasar, da kuma cin hanci da rashawa da aikata laifuka da zagon ƙasa.

Leave a Reply