Ana fargabar zaftarewar ƙasa ta rutsa da mutane da dama a Kenya

2
55

Ana fargabar zaftarewar ƙasa ta rutsa da mutane da dama a Kenya

Ƙungiyar Bayar da Agaji ta red Cross a Kenya ta ce ma’aikatan ceto na ci gaba da ƙoƙarin ceton mutane da dama da zaftarewar ƙasa ta rutsa da su a yankin tsakiyar ƙasar sakamakon samun mamakon ruwan sama.

Zaftarewar ƙasar ta afku a yankin Kimende, in ji sanarwar da Red Cross ta fitar ta shafin X.

KU KUMA KARANTA: Kimanin mutane 30 ne suka mutu a zaftarewar ƙasa a Kamaru

Ya zuwa yanzu ba a bayyana samun rasa rai ba sakamakon lamarin.
Sanarwar ta ce “Jami’an tsaron sun yi wa yankin ƙawanya tare da ayyana shi a matsayin mai cike da hatsari.”

Mamakon ruwan sama da ambaliya na afku wa a ƙasar ta Gabashin Afirka tun ƙarshen watan Maris, inda ibtila’in ya yi ajalin aƙalla mutane 289 tare da raba 285,000 da matsugunansu.

A lamari mafi muni da ya afku, aƙalla mutane 61 ne suka mutu a karshen watan Afrilu, bayan zaftarewar ƙasa da ta biyo bayan ruwan sama a garin Mai Mahiu da ke tsakiyar Kenya.

2 COMMENTS

Leave a Reply