Ana fargabar ‘yan bindiga sun sake ɗiban ɗalibai a jami’ar tarayya ta Dutsinma
Daga Idris Umar, Zariya
‘Yan bindiga sun sake kai hari a Jami’ar Tarayya dake Dutsinma (FUDMA), Jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da wani ɗalibi daga ɗakin kwanan jami’ar. Wannan farmakin ya sake jefa al’umma cikin fargaba, musamman dangane da taɓarɓarewar tsaro a yankin.
Bisa ga bayanan da muka samu, lamarin ya faru ne a daren Talata, wayewar garin Laraba, lokacin da mahara suka kutsa cikin ɗakin kwanan ɗaliban, suka ɗauke ɗaya daga cikinsu. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shigo cikin jami’ar cikin shirin tsaf, tare da cin zarafin dalibai kafin su tafi da wanda suka yi garkuwa da shi.
Wani dalibi da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, “Mun firgita sosai, domin ba wannan ne karo na farko da ‘yan bindiga ke kai hari a jami’ar ba. Muna bukatar hukumomi su ɗauki matakan da suka dace don kare rayukanmu.”
KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a garin Zakirai da ke Kano
Har yanzu ba a samu cikakken bayani ba kan matakin da hukumomin tsaro suka ɗauka, amma rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro na kokarin bin sahun maharan. Shugabancin jami’ar da hukumomin tsaro na jihar sun sha alwashin ɗaukar kwararan matakai don dakile yawaitar irin wannan hare-hare a jami’ar.
Wannan hari na zuwa ne bayan wasu hare-hare da suka gabata a jami’ar, lamarin da ke ƙara jefa iyayen ɗalibai cikin damuwa kan tsaron ‘ya’yansu. Al’ummar yankin da dalibai na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar matakan kawo ƙarshen wannan matsala domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron lafiyar jama’a.