Jami’ar Columbia ta soke zuwa ajujuwa sannan an kama masu zanga-zanga da dama a jami’o’in Yale da New York kuma an rufe ƙofofin shiga Jami’ar Harvard Yard a yayin da ake ɗalibai ke ci gaba da gangamin ƙyamar yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza.
Hukumomi sun ɗauki waɗannan jerin matakai ne ranar Litinin a yayin da a makon jiya aka kama masu zanga-zanga fiye da 100 da ke goyon bayan Falasɗinu waɗanda suka kafa tantuna a jami’ar Columbia.
Baya ga gudanar da zanga-zanga a manyan jami’o’in Amurka, masu gangamin sun gudanar da jerin zanga-zanga a rassan jami’o’in ciki har da Massachusetts Institute of Technology, New York University, da University of Michigan.
Ɗaliban sun buƙaci hukumomin jami’o’in su fito su yi Allah wadarai da mamayar da Isra’ila take yi wa yankin Gaza sannan sun janye daga duk wata yarjejeniya da kamfanonin da ke sayar wa Isra’ila makamai.
Wasu Yahudawa ɗalibai sun ce caccakar da ake yi wa Isra’ila ta sa hankulansu sun tashi.
An yi ta tayar da jijiyoyin wuya ranar Litinin a Columbia da ke Birnin New York, inda aka hana duk mutumin da ba shi da katin shaida, wato ID card shiga jami’ar bayan da tarzoma ta ɓarke a ciki da wajenta.
Wata mata ta jagoranci gomman masu zanga-zanga a titin da ke gefen jami’ar wajen inda suka riƙa rera taken, “A bar Falasɗinawa su sarara!” Ko da yake wani gungun mutane da ke goyon bayan Isra’ila ya gudanar da ƙwarya-ƙwaryar zanga-zanga don yin martani kan masu goyon bayan Falasɗinawa.