Ana ci gaba da gudanar da taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas a jihar Yobe

0
268
Ana ci gaba da gudanar da taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas a jihar Yobe

Ana ci gaba da gudanar da taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas a jihar Yobe

Daga Idris Umar, Zariya

Taron Gwamnonin Arewa Masu Gabas sun fara taron kungiyar gwamnonin, a karo na 11, wanda aka fara da kimanin karfe 11:00 na safiyar ranar Alhamis, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Taron ya samu halartar gwamnonin yankin; Gwamnan Adamawa, Ahmad Umar Fintiri, Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, Bauchi, mataimakin Gwamna- Hon. Auwalu Jatau,

Sa’ilin da yake jawabi kan taron, shugaban kungiyar gwamnonin yankin, kuma Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jaddada bukatar daukin gaggawa wajen magance matsalolin da yankin yake fuskanta, musamman a fannonin karancin abinci, tabarbarewar harkokin sufuri, kiwon lafiya, sannan uwa uba, koma bayan tattalin arziki.

Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda tabarbarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Najeriya, ta fuskacin yaki da matsalolin tsaron, ind ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.”

“Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin jihohinmu wani al’amari ne mai matukar tayar da hankali wanda hakan zai iya kara ta’azzara nasarorin da aka samu a fagen yaki da matsalolin tsaro. Ina mai bayar da shawarar cewa sojojinmu su fadada sabbin dabarun da suke dasu wajen dakile farmakin yan ta’adda.”

KU KUMA KARANTA:Taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas: Dole ne mu ƙarfafa haɗin kai don dakatar da matsalar tsaro – Gwamna Buni

Gwamna Zulum ya ce, “kangin talaucin da yankinmu yake fuskanta, abin tsoro ne, kuma ya zama dole mu dauki ingantattun matakai don magance wannan kalubale. Mu fahimci cewa talauci babbar barazana ne ga tattalin arziki, wanda zai iya shafi zamantakewa.”

“A kokarin nemo madafa, noma kadai ba zai kasance mafita ba, a yaki da talauci. Dole mu kara mayar da hankali kan samar da kyakkyawan yanayi don kafa kananan da matsakaitan masana’antu a yankin mu.”

“Abin ya hada da sa hannun jari a kayayyakin more rayuwa, bayar da fifiko wajen zuba jari mai yawa ga kamfanoni masu zaman kansu, don habaka kasuwanci da kirkire-kirkire.”

Ya ce dole ne su yi aiki don rage talauci ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa tunani tare da tallafa wa kananan masana’amtu, bunkasa kasuwanci, ta fuskar habaka masana’antu, don fadada tattalin arziki tare da samar da dama ga matasa.

Da farko, mai masaukin bakin taron, kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a lokacin da yake jawabin bude taron, ya ce a matsayinsu na Gwamnonin yankin za su yi amfani da dandamalin wajen yanke shawarar da za ta kai ga samar da mafita ga matsalolin da yankin yake fuskanta.

“Irin karfin niyya da kyakkyawan kudurori, shawara mai nagarta, da daukakar mataki a cikin gaggawa, wanda shugabanin mu da suka gabata, ko shakka babu sun haskaka makomar yankin Arewa Masu Gabas.

“Yau ma gashi mun taru domin daukar sabbin kudurori da shawarwari nagari, don bin sawun magabatanmu wajen kawo ci gaba a yankinmu.

Kuma nuna sa ran haɗuwarmu zai fitar da sakamako na gari”

Leave a Reply