Ana buƙatar fiye da matakin Soja wajen samar da tsaro a Najeriya – Babban Hafsan Tsaro
A cewarsa, matakin soja bai wuce kaso 30 cikin 100 na abin da ake buƙata wajen tabbatar da tsaron ƙasa ba, yayin da ragowar kaso 70 din ya dogara a kan matakan zamantakewar siyasa da tattalin arziƙi.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya jaddada cewa daukar matakin soja kadai ba zai samar da tsaro a Najeriya ba.
A cewarsa, matakin soja bai wuce kaso 30 cikin 100 na abin da ake bukata wajen tabbatar da tsaron kasa ba, yayin da ragowar kaso 70 din ya dogara a kan matakan zamantakewar siyasa da tattalin arziki.
Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a kan tsaron Najeriya da muradun kasa, da cibiyar yaki da ta’addanci ta Najeriya karkashin ofishin mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro ta shirya da hadin gwiwar ‘yan jaridu masu daukar rahotannin tsaro, a Abuja.
KU KUMA KARANTA:Ba mu muka ƙara farashin man fetur ba — Gwamnatin Tarayya
Babban hafsan tsaro wanda ya yi sharhi a kan maudu’i mai taken, “tsaro da muradun kasa: yadda ‘yan jarida za su rika ba da rahotannin ci gaba a harkar tsaro,” ya jaddada bukatar hada karfi wajen tunkarar matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Janar Musa ya kara fayyace rawar da aikin jarida zai iya takawa wajen inganta tsaro a kasar.
Ya kara da cewa za a iya inganta kokarin soji na kare martabar Najeriya ta hanyar aikin jarida na ci gaba wanda wani tsarin jarida na musamman dake maida hankali a kan ci gaban zamantakewa da tattalin arziki har ma da siyasa.