Ana barazana ga rayuwata, ɗan takarar gwamna a Legas ya koka

Ɗan takarar gwamnan jihar Legas a ƙarƙashin jam’iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour, ya koka kan barazanar da ake yiwa rayuwarsa dama yunƙurin kashe shi.

Gbadebo ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Arise a ranar Lahadi, inda ya ce an kai masa hari ranar Asabar.

Ya ce, “Akwai barazana da yawa, mun samu bayanai da yawa game da yuwuwar yunkurin kisan gilla a rayuwata. Eh, hakan ya faru ne a yankin Epe.

“Mun samu Honorabul Wale Oluwo tare da mu kuma Honorabul Najid na jam’iyyar PDP da ke aiki tare da mu, duk an harbe su jiya a Epe.” In ji shi.

KU KUMA KARANTA: Ban janye takarata ba, inji ɗan takarar gwamnan jami’yyar NNPP a Ogun


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *