An ɗaure ɗan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda fyaɗe

An ɗaure ɗan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda fyaɗe

An ɗaure ɗan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda fyaɗe

Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zamanta a Akure ce ta yanke wa yaron hukunci ne bayan an tabbatar da laifin.

An fara gurfanar da wanda aka kama da laifin ne a watan Disambar 2021, bisa tuhume-tuhume biyu na cin zarafi da fyade, wanda a wancan lokacin yaron ya ki amsa laifinsa.

Lauyan mai shigar da ƙara, Dayo Kayode, ya sanar da kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 11 ga Maris 2021, da misalin karfe 5 na yamma.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta tura wani gidan yari kan yi wa ’yar shekara 50 fyaɗe

A cewar masu gabatar da ƙara, laifukan sun ci karo da sashe na 60, da na 358 na kundin laifuffuka na Jihar Ondo, na shekarar 2016.

Da yake sanar hukuncin, Mai Shari’a Yemi Fasanmi, ya yanke wa yaron hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari bisa kan laifin cin zarafi.

Sannan ya aka yanke masa shekaru 12 a gidan yari bisa laifin aikata fyaɗe.

“Jimillar ɗaurin shekaru 14 a gidan yari zai fara ne daga ranar farkon da aka kama wanda aka yanke wa hukuncin,” in ji Alkalin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *