No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ƙaddamar da dokar ta-ɓaci game da satar waya da kuma wasu laifukan da ake aikatawa a birnin.

Kafofin yaɗa labarai sun ce majalisar dokokin jihar ta nuna damuwa kan matsalolin satar waya da sane da shan miyagun ƙwayoyi da ma waɗansu laifukan da ke barazana ga zaman lafiyar jihar.

A wata mahawara da shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar, ‘yan majalisar sun amince kan cewa akwai buƙatar a gaggauta magance matsalar kafin ta yi ƙamari.

KU KUMA KARANTA: “Idan na saɓa rantsuwar da na yi, babu lauyan da zai kare ni a cikin kabari” – Gwamnan Kano

Majalisar dokokin ta kuma amince da wani ƙuduri da ya buƙaci gwamnatin jihar ta ɗauki dukkan matakan da suka kamata domin hukunta waɗanda aka kama da laifi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...