Connect with us

Labarai

An yiwa kalamai na gurguwar fahimta – Kashim Shettima

Published

on

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya nesanta kansa da wasu kalamai da ya ce “ba daidai ba ne, kuma masu hatsari” da wasu ke alaƙantawa da shi.

Wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran mataimakin shugaban ƙasar ya fitar, ta ruwaito Kashim Shettima na cewa kalaman da ake ambatawa ya furta lokacin wani taro da sanatoci ranar Lahadi wasu masu jamhuru ne suka kitsa a yunƙurinsu na nuna rashin dacewar ‘yan takara Musulmai da ke neman shugabancin Majalisar dattijai.

Sanarwar ta zo ne bayan wani bidiyo da ke ta yawo a shafukan sada zumunta wanda a ciki aka jiyo Kashim Shettima lokacin gabatar da jawabi, yana cewa “A wajena idan ana maganar wannan gwamnati, Kirista mafi lalacewa kuma mafi rashin ƙwarewa daga Kudancin Najeriya, ya fi Musulmin Arewa na-ƙwarai a kan muƙamin shugaban majalisar dattijan tarayyar Najeriya”.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Tinubu, ba za ta musuluntar da Najeriya ba – Shettima

Ya ce ba a bayyana kalaman a muhallin da aka yi su ba, kuma an canza musu ma’ana don kawai su dace da manufar masu zagon ƙasa ga burin al’ummar Najeriya na tabbatar da haɗin kan ƙasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a yayin taron da ‘yan majalisar dattijai masu gangamin ganin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin sun jagoranci majalisar dattijai ta goma, Kashim Shettima ya jaddada tsarin siyasar ƙasar inda ya yi nuni da cewa samun Kirista daga kudancin Najeriya da kuma wani Musulmi daga Arewaci shi ne zai tabbatar da daidaiton adalci don inganta muradin shigar da kowa a dama da shi a gwamnatin tarayya.

Ta ce kalaman Sanata Kashim Shettima sun taso ne sanadin wani gagarumin gangami game da rarrabuwar da ke tsakanin al’ummar ƙasar, kuma sun dace da alƙawarin jam’iyya mai mulki na ganin an dama da kowa a dukkan lardunan da rukunonin al’umma.

Ta ambato Sanata Shettima yana nunar da cewa, bisa la’akari da ganin shugaban Najeriya da mataimakinsa duk Musulmai ne, to ba zai kasance rashin kan gado ga ‘yan majalisar ba, idan suka zaɓi ɗan takarar da ba Musulmi ba, ko da kuwa akwai Musulmin da ya fi cancanta, saboda tabbatar da daidaito.

A cewarsa, abin fargaba ne idan aka jirkita irin wannan roƙo maras harshen damo don nunar da cewa mataimakin shugaban ya ce duk lalacewar Kirista ya fi ɗan takara Musulmi.

Kashim Shettima ya ce rashin kan gado ne ma a ce mataimakin shugaban ƙasar wanda shi kansa Musulmi ne, zai iya ƙasƙantar da ƙwarewar ɗan’uwansa Musulmi a ƙasar da Musulmi ke jagoranta, har ma ya nuna nagartar shugabancin da babu kamarta, bisa doron da aka zaɓe su ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a watan Fabrairun da ya wuce.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Shettima ya jagoranci taron majalisar tattalin arziƙin ƙasa | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like