An yi zanga-zanga a fadar Sarkin Zazzau kan matsalar tsaro

Daga Maryam Umar Abdullahi

Al’ummomin ƙaramar hukuma Giwa a Jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zanga a Faɗar Sarkin Zazzau kan matsalar ke addabar yanƙinsu.

Matasa da dattijai da yara daga yankin Tumburku da ke gundumar Galadimawa ne suka gudanar da zanga-zangar lumana a kofar fadar Sarkin Zazzau domin gabatar da korafin dangane da rashin tsaro da ke addabar su.

Sun gudanar da zanga-zangar ne washegarin da ’yan bindiga suka kashe wasu mutum biyu, suka kuma yi garkuwa da wasu 26 a yankin ƙaramar hukumar.

Jama’ar sun yi dafifi ne a kofar fada tare da roƙon Sarkin Zazzau ya sanya baki tare da gabatar da koken su kan hare-haren ’yan bindiga da kusan a kullum suke addabar su.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari wani sansanin soji a jihar Katsina

Ɗaya daga cikinsu, Amiru Abubakar ya ce, yawancinsu manoma ne kuma masu iyali, amma sun bar yankin saboda yadda kullum sai an yi jana’izar mutane da ’yan bindigar suke kashewa.

Ya bayyana rayuwar da halin da suke ciki a matsayin na rashin tabbas da tashin hankali.

“Irin noman da muke yi a yankin ya isa mu ciyar da Jihar Kaduna, amma yanzu kowa ta kansa yake da neman abin da zai sa a bakin Salati”, a cewar Amiru.

Shi kuma, Shamsudeen Hamza Imam, ya ce sun zo fadar Sarkin ne da nufin su roke shi ya sa baki tare da ƙira ga hukumomin da lamarin ya shafa su taimaka musu da jami’an tsaro daga yankin Galadimawa har zuwa Tumburku domin kare lafiya da duƙiyoyinsu.

A cewar Shamsudin, babu sana’ar da suka iya banda noma da kiwo, amma yanzu noman ya gagare su.
Ya ce mutanen su sun watsu a wurare masu daban-daban inda suke gudun hijira, kuma suna cikin mawuyacin hali yanzu haka.

Shi ma Muhammad Mukhtar Tumburku na gundumar Kidandan, ya ce masu garkuwa da mutane na addabar su kowane lokaci kuma abin na damun su matuƙa.

Shi ma ya roƙi Sarkin Zazzau ya taimaka wurin isar da saƙonsu ga dukkanin hukumomin da lamarin ya rataya a kansu.

Jama’ar yankin sun roƙi Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani da kuma dukkan masu ruwa da tsaƙi a bangaren tsaro su taimaka wajen ganin yanƙin nasu ya samu zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.

Da yake maida jawabin, Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, wanda ba ya gari lokacin da suka zo fadan, amma ya yanƙe taron da suke da Gwamnan Kaduna a kan tsaro don dawowa Zariya ya gana da masu zanga-zangar lumana.

Ya jajanta masu kan rayuƙan da aka rasa, sannan ya tabbatar masu cewa ana daukar matakan da suka kamata yanzu haka, don shawo kan matsalolin.

“Kodayaushe haƙimin ku, shi Kaigaman Zazzau kan zo don sanar mana halin da ake ciki, kuma ana ɗaukar matakan da suka kamata don samar da tsarin tabbatar da tsaro a yankin”, a cewar Sarkin Zazzau.

Ya yi fatan jama’ar za su koma don cigaba da daukar matakan da suka kamata tsakanin al’ummominsu tare da taimaka wa ƙoƙarin hukumomi na samar da cikakken tsaro a yankunan ƙarkara da birane.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *