An yi wa tsohon shugaban ƙasar Sierra Leone Koroma ɗaurin-talala

0
116

An yi wa tsohon shugaban ƙasar Saliyo Ernest Bai Koroma ɗaurin-talala bayan an yi masa tambayoyi game da abin da gwamnatin ƙasar ta bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki a ƙarshen watan Nuwamba.

Sai dai ofishin tsohon shugaban ƙasar, wanda ya jagoranci Saliyo daga 2007 zuwa 2018, ya ce ba a yi masa ɗaurin-talala ba.

Ministan Watsa Labarai Chernor Bah ya ce Koroma, wanda a ranar Juma’ar da ta gabata aka yi masa tambayoyi, an sake gudanar da bincike a kansa ranar Asabar sannan aka sake shi bisa “sharaɗin cewa ba zai fita daga gidansa ba”.

“Ba zai iya fita daga gidansa ba sai da izinin shugaban ‘yan sandan Saliyo, in ji Bah a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

Bah ya ƙara da cewa daga yanzu za a bar mutum uku ne kaɗai su ziyarci Koroma daga iyalansa da kuma jami’an jam’iyyarsa — kuma sai shugaban ‘yan sanda ya amince kafin su gana ranar Litinin.

KU KUMA KARANTA: An kama tsohon shugaban mulkin sojan Guinea da ya tsere daga gidan yari

A sanarwar da ofishin Koroma ya fitar, ɗaya daga cikin lauyoyinsa ya musanta cewa ana yi masa ɗaurin-talala sai dai ya ce “an ƙara yawan jami’an tsaro a kusa da gidansa da kuma titunan da ke hanyar gidan”.

Ranar Alhamis ɗin da ta gabata aka tura wa Koroma sammaci domin ya hallara a ofishin ‘yan sanda da ke Freetown cikin awa 24, a wani ɓangare na bincike bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan jiya.

Da sanyin safiyar ranar 26 ga watan Nuwamba ne wasu ɗauke da makamai suka kai hari a rundunar soji da barikin soji biyu da gidajen yari biyu da manyan ofisoshin ‘yan sanda biyi, inda suka yi gumurzu da jami’an tsaro.

Lamarin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 21, a cewar Ministan Watsa Labarai na ƙasar Chernor Bah.

Tun daga lokacin an kama aƙalla mutum 71 bisa hannu a abin da Shugaba Bio ya bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki.

Leave a Reply