No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu da ake zargin ’Yan Kalare ne sun yi wa wata mata mai ’ya’ya takwas yankan rago a garin Gwambe.

Maharan sun shiga gidan Malama Aishatu Abdullahi mai shekaru 58 ne a daren Juma’a, suka yi mata yankan rago a unguwar Jekadafari.

Wani rahoto da Aminiya ta samu daga hadimin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya kan sha’anin tsaro da harkokin gwamnati, Ambasada Yusuf Musa Danbayo, ya ce ana kyautata tsamnanin turo su aka yi su kashe matar.

Ya bayyana cewa maharan sun shiga gidan Malama Aishatu ne da misalin ƙarfe 9 na dare aka yi mata yankan rago sannan suka tsere da wayar salularta.

Hadimin gwamnan ya ce bayan faruwar lamarin an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka ziyarci gidan suka ɗauke ta zuwa asibitin ƙwararru na jihar.

Kakakin ’yan sandna jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce a lokacin da ’yan sandan suka isa gidan marigayiyar sun tarar da ita kwance male-male cikin jini, suka ɗauke ta zuwa asibitin inda a nan ne likita ya tabbatar da mutuwar ta.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Zamfara sun kama waɗanda ake zargi da kisan ɗan jarida a jihar

Jami’in ya ce, kwamishinan ’Yan Sanda Mai Kula da Ayyukan, Hayatu Usman a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar, ya ba da umarnin a gagguata fara bincike don gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Ya ƙara da cewa rundunar ba za ta zauna ta naɗe hannu miyagun abubuwa irin haka na faruwa ba, don haka sai sun zaƙulo waɗanda suka aikata laifin dan fuskantar shari’a.

Daga nan sai yace dokar nan da aka sanya ta taƙaita zirga- zirgar jama’a daga ƙarfe 12 na dare ta na nan ba canji.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...