An yi wa fursunoni 72 afuwa a gidajen yarin Zariya

0
117

Fursunoni 72 da ke ɗaure a kurkuku a yankin Zariya a Jihar Kaduna sun samu afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa mutum 4,068 domin rage cunkoso a gidajen yari.

Fursunoni 48 aka saki daga gidan gyara hali na Zariya sai 5 daga gidan gyara hali na Ikara sai 19 daga gidan gyara hali na Soba da kuma 19 daga gidan gyara hali na Makarfi.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo wanda ya sami wakilcin mashawarcinsa a fannin shari’a, Barista John Otuko ya shawarci waɗanda aka yafe wa da su kasance masu da’a da nisantar aikata laifi da zai dawo da su gidan gyara hali.

Dokta Olubunmi Tunji-Ojo ya kuma shawarcesu da su yi amfani da abubuwan da suka koya na sana’o’i a lokacin inda suka koma cikin al’ummarsu.

KU KUMA KARANTA: An saki dubban fursunoni don rage cunkoso a gidajen yari

Tun da farko, Kwamandan mai kula da gidajen gyara hali a jihar Kaduna, Ado Saleh ya ce baya ga biyan kuɗin tara da Shugaba Ahmed Tinubu ya yi musu, ya kuma ba su naira dubu 10 kowannensu domin yin kuɗin motan zuwa garuruwansu.

Ya kuma gargaɗesu da su kasance masu hali na gari domin kiyaye faɗawa cikin irin halin da suka tsinci kansu.

Wasu daga cikin waɗanda aka sakin sun bayyana nadamarsu tare da rokon Allah Ya kare su daga aikata dukkan wani laifi da zai dami al’umma.

Leave a Reply