‘Yan fim sun nemi ‘yansanda su gaggauta sakin Jaruma Khadija Mai Numfashi

0
166
'Yan fim sun nemi 'yansanda su gaggauta sakin Jaruma Khadija Mai Numfashi
Khadijah Mai Numfashi

‘Yan fim sun nemi ‘yansanda su gaggauta sakin Jaruma Khadija Mai Numfashi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ƙungiyar Masu Shriya Finafinai ta Arewa (AFMAN) ta nemi Hukumar ’Yan Sandan Ƙasar nan ta gaggauta sakin matashiyar jarumar nan Khadija Mai Numfashi, wadda aka kama a Kano sannan aka kai ta birnin Legas.

Wannan na kunshe ne ta cikin buɗaddiyar wasikar da shugaban ƙungiyar, Salisu Mohammed Officer, ya rubuta wa Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa a ranar Asabar 25 ga Oktoba 2025.

Ƙungiyar ta bayyana damuwa kan yadda aka tsare jarumar ba bisa ƙa’ida ba bisa zargin batanci da wani Kabiru Musa daga Legas ya yi.

KU KUMA KARANTA: Jarumar Kannywood Maryam Muhammed ta roƙi kotu ta raba auren ta da mijinta

AFMAN ta ce hakan ya saba wa ’yancin dan adam da kuma doka, musamman ganin shekarunta bai haura 18 ba in ji wasiƙar.

Kungiyar ta bayyana cewa jarumar marainiya ce da ke ƙarƙashin kulawar mahaifiyarta, kuma ta shiga harkar finafinai ne da jagorancin ƙungiyar ba kara zube ba.

Don haka AFMAN ta yi kira da a binciki lamarin yadda ya kamata tare da tabbatar da gaskiya da adalci.

Ƙungiyar ta kuma bukaci babban sufeton ’yan sanda da ya sa baki wajen ganin an saki jarumar tare da kare ta daga duk wata barazana da take fuskanta.

Tun a ranar Jumuʼa 24 ga Oktoban 2025 ne Yan Sanda suka kama jarumar a Kano sannan suka tafi da ita birnin Legas, bayan wasu cece-kuce da suka yi a TikTok tsakaninta da wata ƙawarta Marwat Dallatu yar jihar Katsina a nan ne batun shi Kabiru Legas ya fito.

Leave a Reply