Tinubu ya sallami hafsoshin tsaro na ƙasa tare da maye gurbin su da wasu
Shugaba Bola Tinubu ya sallami manyan hafsoshin tsaron ƙasa domin ƙarfafa tsaro da kuma rage damuwa kan kan cunkoson ƙarin matsayi a rundunar sojoji.
Wadanda abin ya shafa sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojin kasa, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla; da kuma Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar.
Sai dai kuma Tinubu ya nada Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Babban Hafsan Tsaro domin maye gurbin Janar Christopher Musa. Sabon Babban Hafsan Soja shi ne Manjo-Janar W. Shaibu, AVM S.K. Aneke shi ne sabon Babban Hafsan Sojin Sama, yayin da Rear Admiral I. Abbas shi ne sabon Babban Hafsan Sojin Ruwa.
KU KUMA KARANTA: Shugaban Najeriya ya kori manyan hafsoshin tsaron ƙasar
A wata sanarwa daga Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan hada labarai na al’umma, Sunday Dare, shugaban ƙasa ya kuma bayyana godiya ƙwarai da gaske ga tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da sauran hafsoshin tsaro saboda hidimar ƙasa da jajircewar su wajen jagoranci.









