Gwamnan Bauchi ya naɗa babban yayansa a matsayin Sarki mai daraja ta ɗaya

0
153
Gwamnan Bauchi ya naɗa babban yayansa a matsayin Sarki
Alhaji Adamu Mohammed, Sarkin Duguri

Gwamnan Bauchi ya naɗa babban yayansa a matsayin Sarki mai daraja ta ɗaya

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya naɗa babban yayansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin masarautar Duguri.

Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Aminu Hammayo, ne ya mika wa sabon sarkin takardar naɗin sa a madadin gwamnan a wani bikin da aka gudanar a fadar sarkin Duguri, ƙaramar hukumar Alkaleri, ranar Juma’a.

Yayin bikin, Sakataren Gwamnatin ya shawarci sabon sarkin da ya ci gaba da ba da goyon baya ga manufofi da shirye-shiryen gwamnati domin samun ci gaba mai ɗorewa.

A cikin jawabin sa, sabon sarkin ya gode wa Gwamna Bala Mohammed bisa wannan girmamawa da ya yi masa, inda ya roƙi Allah ya saka masa da alheri.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Bauchi ya dakatar da kwamishinar harkokin mata

Sarkin ya yi alkawarin kasancewa mai biyayya ga Gwamnatin Jihar Bauchi da kuma Majalisar Masarautar Bauchi.

Haka kuma, Aminu Hammayo ya mika takardar naɗi ga sabon Sarkin Masarautar Bununu, Alhaji Jibrin D. Hassan.

Hammayo ya shawarci sabon sarkin da ya yi aiki bisa doka da oda domin samun ci gaba mai ɗorewa tare da haɗa kan kabilu daban-daban don tabbatar da zaman lafiya da bin doka a kowane lokaci.

Jaridar Daily Trust ta rawaito yadda gwamnan ya rattaɓa hannu kan dokar kafa sababbin masarautu 13 a jihar.

Leave a Reply