Majalisar tarayya na nazarin ƙirƙirar sababbin jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278

0
130
Majalisar tarayya na nazarin ƙirƙirar sababbin jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278

Majalisar tarayya na nazarin ƙirƙirar sababbin jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278

Majalisar Tarayya ta fara tattaunawa kan sabon kudiri na gyaran kundin tsarin mulki wanda zai iya kaiwa ga ƙirƙirar sababbin jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278 a faɗin ƙasar.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ke jagorantar kwamitin sake duba kundin tsarin mulki, ya bayyana haka a lokacin wani taron kwamitocin Majalisar Dattawa da ta Wakilai a Legas.

KU KUMA KARANTA: Tinubu yana so a yi zaɓe na gaskiya a 2027 – Kakakin Majalisar Tarayya Abbas

Barau ya ce majalisar ta shafe shekaru biyu tana gudanar da tattaunawa da al’umma da masu ruwa da tsaki, kuma yanzu an tattara kudiri 69, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi da ƙananan hukumomi da gyaran iyakoki.

Ya bayyana cewa burin su ne a mika farkon gyare-gyaren kundin tsarin mulki ga majalisun dokokin jihohi kafin ƙarshen shekara, tare da kira ga ‘yan majalisa da su yi aiki da kishin ƙasa da haɗin kai.

Wannan sabon yunkuri na zuwa ne bayan yunkuri da dama da suka gaza a baya saboda rashin jituwa tsakanin jihohi da ra’ayoyi na siyasa, duk da cewa wasu gyare-gyare kamar ’yancin kuɗi ga majalisun jihohi da bangaren shari’a sun samu nasara.

Leave a Reply