Rikici ya ɓarke tsakanin Akpabio da Natasha a majalisar dattawa kan ƙudirin zubar da ciki

0
159
Rikici ya ɓarke tsakanin Akpabio da Natasha a majalisar dattawa kan ƙudirin zubar da ciki

Rikici ya ɓarke tsakanin Akpabio da Natasha a majalisar dattawa kan ƙudirin zubar da ciki

An samu ɗan rikici a zauren majalisar dattawa a ranar Talata yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya suka yi sabani yayin muhawara kan kudirin gyaran dokar aikata laifuka da ke neman tsananta hukunci ga masu taimakawa wajen zubar da ciki.

Kudirin da Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, na neman ƙara hukuncin daga shekaru uku zuwa goma a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba. Sai dai wasu ’yan majalisa sun nuna damuwa cewa hakan na iya hana likitoci taimakon gaggawa a lokutan da rayuka ke cikin haɗari.

Akpabio ya dakatar da tattaunawar, ya kuma umarci kwamitin majalisar kan shari’a da doka da su sake nazarin kudirin cikin makonni biyu.

KU KUMA KARANTA: Me ya hana Sanata Natasha dawo wa majalisa, bayan lokacin dakatarwar da aka mata ya ƙare?

Sai dai bayan an dakatar da batun, Sanata Natasha ta nemi damar yin magana tana mai cewa batun ya shafi mata kai tsaye, amma Akpabio ya hana ta magana, yana mai cewa an rufe muhawarar gaba ɗaya.

Sanata Adams Oshiomhole ya goyi bayan matakin Akpabio, yana cewa sake buɗe batun zai karya dokokin majalisar.

Bayan zaman, Natasha ta bayyana takaici cewa an hana ta yin magana kan batu da ya shafi haƙƙin mata da lafiyarsu, tana mai cewa za ta bayar da gudunmawa lokacin da kwamitin majalisar zai sake nazarin kudirin.

Leave a Reply